Rasuwar Maman Taraba: Nijeriya Ta Yi Rashin 'Yar Kishin Kasa -Farfesa GwarzoShugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British International University daje Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bayyana rasuwar tsohuwar ministan harkokin mata, Hajiya Jummai Alhassan a matsayin babban rashi ga Nijeriya. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya bayyana hakan ne a cikin takardar ta'aziyya da ya aiko daga birnin Paris zuwa ga iyalai da 'yan'uwan Marigayiyar kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin. 

Tsohuwar ministar dai ta rasu ne a birnin Cairo ta kasar Misra bayan ta yi fama da rashin lafiya, inda tuni aka bizneta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinta wato Jalingo ta jihar Taraba. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya bayyana rasuwar tsohuwar ministan harkokin matan wacce aka fi sani da 'Maman Taraba', a matsayin cewa 'yan Nijeriya sun rasa mace jajirtacciya 'yar siyasa wacce ta sadaukar wajen kwatar 'yancin mata a cikin al'ummarta. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya ce ya san Marigayiya Jummai Alhassan a matsayin tsayayyiyar mace kuma 'yar kishin kasar Nijeriya wacce za a ci gaba da tunawa da ita na tsawon lokaci a fadin kasar. 

"'yan Nijeriya za su kwashe tsawon lokaci suna tunawa da tsohuwar ministan harkokin matan a matsayin mai kishin Nijeriya", inji shi. 

Ya ci gaba da cewa; "ina son amfani da wannan damar wajen mika sakon ta'aziyyata ga iyalai da 'yan'uwan tsohuwar ministan tare da al'ummar jihar Taraba da ma 'yan Nijeriya baki daya bisa wannan babban rashin da aka yi", ya nusasshe. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya karkare da yiwa Marigayiyar addu'a, inda ya roki Allah da ya sanya ta a Aljannah Firdaus, sannan kuma ya bai wa iyalai da 'yan'uwan Marigayiyar hakurin jure wannan babban rashin da aka yi. 


Post a Comment

0 Comments