Sallar Idi Na Nan Daram A Gidan Sheikh Dahiru Bauchi A Yau LarabaA bisa bayanan da wasu suka kama yadawa na cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a cigaba da Azumi, batun ba gaskiya ba ne.

Almajirin Shehin sun tabbatar da cewa wasu makiya ne da batun Sallar Idi a Yau Laraba bai musu dadi ba suka kama yadawa domin karkatar da hankalin jama'a.

"Mu yanzu muna kan shirin Sallar Idi ne kamar yadda aka sanar tun jiya. Muna sake nanata batun Sallar Idi da karfe 9:30," Inji Hadimin Shehin.

Sun tabbatar da cewa Sallar Idi na Nan karfe 9:30 ma safiya.

Post a Comment

0 Comments