Sarkin Musulmi Ne Ke Da Hakkin Sanar Da Tabbatar Ganin Wata, Inji Sheikh JaloDaga Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo 

1. Abin da aka sani a Shari'ar Musulunci shi ne: Sarkin Musulmi shi ke da hakkin bayyanar da ranar daukan azumi ko ranar ajiye azumi cikin kasarsa a duk lokacin da ganin wata ya tabbata a gurinsa ta daya daga cikin hanyoyin tabbatar tsayuwar wata a cikin addinin Musulunci. 

Hujjar wannan bayani shi ne: hadithan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da suka tabbata cikin wannan babi kamar:-

- Hadithin Abu Dawud na 2,342, daga Sahabi Abdullahi Bin Umar cewa:-
((تراءى الناس الهلال فأخبرت رسول الله صلى الله عليه وسلم: أني رايته، فصام وأمر الناس بصيامه))
Ma'ana: ((Mutane sun dubi jinjirin wata sai na ba wa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata gare shi tare da iyalan shi- labarin cewa na gan shi, sai ya yi azumi, ya kuma umurci mutane da su azumce shi)). 

- Hadithin Abu Dawud na 1,339, da Baihaqiy cikin Sunnan na 8,447, daga Rib'ii Bin Hirash daga wani mutum cikin Sahabban Manzon Allah cewa:
((قد اختلف الناس في اخر يوم رمضان، فقدم اعرابيان فشهدا عند النبي صلى الله عليه وآله وسلم: لأهل الهلال أمس عشية، فأمر رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم الناس ان يفطروا)).
Ma'ana: ((Hakika mutane sun yi ta sassabawa a karshen Ramadan, sai wasu kauyawa biyu suka zo suka ba da shaida a gaban Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi tare da iyalan shi cewa: Wallahi jinjirin wata ya tsaya jiya da yamma, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi tare da iyalan shi ya umurci mutane da su sha ruwa)). 

2. A cikin wadannan Hadithai kamar yadda kuke gani Annabi ne a matsayinsa na shugaban Al'umma kuma shugaban daularsu yake ba da umurnin daukan azumi da ajiye shi; wannan shi ne ya sa Babban Malamin Sunnah Ibnu Qayyimil Jauziyyah ya ce cikin littafinsa Zaadul Ma'ad 2/49:
((وكان من هديه صلى الله عليه وآله وسلم امر الناس بالصوم بشهادة الرجل الواحد المسلم وخروجهم منه بشهادة اثنين)).
Ma'ana: ((Ya kasance daga cikin al'adar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi tare da iyalan shi: umurtan mutane da yin azumi idan Musulmi daya ya ba da shidar ganin watan Azumi' da kuma umurtansu da yin sallar Idi idan Musulmi biyu suka ba da shaidar ganin watan Shawwal)).

3. Bayanan malaman mazhabobin fiqhu cikin wannan mas'ala:

- A mazhabar Hanafiyyah Ibnu Aabidin ya ce cikin Haashiyatu Raddil Muhtar 2/388: 
((والصحيح من هذا كله انه مفوض الى رأي الامام ان وقع في قلبه صحة ما شهدوا به وكثرت الشهود امر بالصوم)).
Ma'ana: ((Ingantacciyar magana ita ce: Harkar tabbatar jinjirin wata abu ne da ake jingina shi zuwa ga Sarkin Musulmi, duk lokacin da ganin wata ya inganta a wurinsa, kuma shaidu suka yawaita to sai ya yi umurni da a yi azumi)).

- A mazhabar Malikiyyah Ibnu Rushd ya ce cikin Al-Muqaddimaatul Mumahhidat 1/251:-
((فإذا ثبت عند الامام روية الهلال بشهادة عدلين امر الناس بالصيام او الفطر وحمل الناس عليه)).
Ma'ana: ((Idan ganin jinjirin wata ya tabbata a wurin Sarkin Musulmi da shaidar adilai biyu to sai ya umurci mutane da yin azumi, da kuma yin idin azumi, kuma ya tilasta wa mutane yin hakan)).

- A mazhabar Hanbaliyyah, ya zo cikin littafin Masaa'ilu Imam Ahmad Bi Riwayati Abdillah 2/610-611:-
((سالت ابي عن روية الهلال اذا شهد على رؤيته رجل واحد؟ فقال: يأمر الأمير الناس بالصيام)).
Ma'ana: ((Na tambayi babana game da ganin jinjirin wata idan mutum daya ya ba da shaidar ganinsa? Sai ya ce: Sarkin Musulmi sai ya umurci mutane da yin azumi)).

4. Fatawar Bin Baz cikin mas'alar:
Sheik Bin Baz ya ce cikin Majmuu'ul Fataawa 15/97:-
((اما الأفراد من المسلمين فعليهم أن يصوموا تبعا لقادتهم ويفطروا معهم؛ لقول النبي صلى الله عليه وسلم: الصوم يوم تصومون والفطر يوم تفطرون والأضحى يوم تضحون)).
Ma'ana: ((Amma su daidaikun mutane Musulmi wajibi ne a kansu su yi azumi ko su sha ruwa a lokacin da shugabanninsu suka ce a yi haka, saboda Hadithin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah: "Azumi shi ne ranar da kuke azumi, Idin karamar salla ranar da kuke Idin karamar salla, Idin Layya ranar da kuke Idin Layya")).

5. Muna fata 'yan'uwa Musulmi za a daure a rika yin Musulunci kamar yadda ya tabbata cikin Shari'a. Muna rokon Allah Ya nuna mana wannan wata na Ramadan lafiya Ya ba mu ladan da ke cikinsa, Ya tabbatar da mu a kan sunnar Annabi cikin Aqida, da Ibada, da Mu'amala. Ameen.

Jibwis Nigeria

Post a Comment

0 Comments