Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Jami'ar MAAUN Ya Taya Juliana Bitrus Murna Bisa Samun Mukamin Kwamishinan Lafiya A Jihar Borno

Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British International University, dake Ka...Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British International University, dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya Juliana Bitrus bisa samun mukamin Kwamishiniyar lafiya da ayyukan al'umma a jihar Borno. 

Bitrus ta kasance kwamishinar lura da dabbobi da ci gaban harkokin kifi kafin daga bisani a maidata ma'aikatar lafiya da ayyukan al'umma a sake fasalin gwamnatin da gwamnan jihar ya yi a ranar Talata. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya taya Juliana Bitrus murna ne a sakon da ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Talata. 

Juliana Bitrus ta kasance tsohuwar daliba ce a Jami'ar ta MAAUN. 

"ina son taya Juliana Bitrus murna, wacce ta kasance dalibar da ta karanci bangaren lura da lafiya (Nurse/Midwife) kuma ta zama kwamishinar lafiya a jihar Borno", inji Farfesa Abubakar. 

Ya yi addu'ar Allah ta'ala ya bata kariya tare da bata fasahar gudanar da ayyukan da aka dora mata a matsayin kwamishinar lafiya da ayyukan al'umma. 

Har wala yau a sakon ya nemi sabuwar Kwamishinar da ta zama jakada ta gari ga Jami'ar da ta kammala wajen gudanar da aikinta cikin tsoron Allah. 

"A madadin hukumar dake gudanar da Jami'ar MAAUN, ina son sake amfani da wannan dama wajen taya ki murna bisa sabon mukamin da aka ba ki tare da miki addu'ar samun nasara, taimakon Allah da kuma kariya ta musamman a dukkanin abin da kika sanya a gaba," inji Farfesa Abubakar Gwarzo.

No comments