Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyoyin Matasa Sun Gudanar Gangamin Nuna Alhini Ga Ƴan Nijeriya A Kano

Sakamakon matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan wanda hakan ya sanya dubban al’umma su ka rasa rayukansu tare da asarar dukiya ta Miliyoyin ...


Sakamakon matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan wanda hakan ya sanya dubban al’umma su ka rasa rayukansu tare da asarar dukiya ta Miliyoyin Naira a dalilin rikice – rikice da kuma taɓarɓarewar tsaro, ya sanya gamayyar ƙungiyoyin matasa a jihar Kano su ka yi gangamin addu’a tare da alhini ga waɗanda su ka rasa rayukansu.

Tun da farko jagoran kungiyoyin matasan Aliyu Dahiru Aliyu ya bayyana cewa sun zaɓi ranar 28 ga watan Mayun kowacce shekara a matsayin ranar alhini tare da juyayi ga ƴan Najeriyar da su ka rasa rayukansu.Matasan da su ka yi macin cikin bakaken riguna mai ɗauke da wani rubutu cikin harshen turanci ‘Nigeria Bleeds’ ma’ana Malalar Jini A Najeriya.

A lokacin gangamin an fara da jawabai akan irin matsalolin tsaro da su ka addabi ƙasar nan tare kuma da karanto wasu daga cikin sunayen waɗanda suka rasu sakamakon matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Haka kuma matasan sun yi addu’ar neman samun rahamar ubangiji ga Musulman da su rasu tare kuma da yin shiru na tsahon minti ɗaya domin nuna girmamawa ga mamatan.

A ƙarshe jagoran gangamin Aliyu Dahiru Aliyu ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara azama wajen magance matsalar tsaro da ke ƙoƙarin gagarar Kwandila tare kuma da buƙatar gwamnati da ta ayyana ranar 28 ga watan Mayun kowacce shekara a matsayin ranar nuna Alhini ga ƴan Najeriyar da su ka rasa rayukansu.

Matsalar Tsaro A Najeriya

Babu shakka girman matsalar tsaro na ci gaba da ƙonawa jama’a gyaɗa a tafin hannu a Najeriya, lamarin da ya sanya ƴan Najeriya da dama su ka yanke ƙauna daga alƙawarin da jam’iyyar APC da gwamnatin shugaba Muhammad Buhari su ka yi musu a lokacin yaƙin neman zaɓe a shekarar 2015.

Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta gudanar a ƴan watannin baya, ya bayyana yadda wadannan ƴan bindiga suka tashi garuruwa da dama a Jihar Kaduna waɗanda yanzu haka suka zama kufai, wato babu kowa a cikin su, abinda ya tilastawa mazauna wadannan garuruwa komawa birane domin tsira da rayukan su.

Hare haren ƴan bindiga, musamman a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Neja da Nasarawa da kuma Benue sun yi sanadiyar rasa daruruwan jama’a da kuma jikkata wasu da dama, a ɗaya ɓangaren kuma batun garkuwa da mutane domin karbar kuɗin fansa ya zama tamkar ruwan dare a yankunan arewacin Najeriya.

Najeriya dai na fuskanyar matsalar tsaro da tashe-tashen hankali a kusan dukkan sassan kasar nan, kama daga hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas, da ayukan Fulani ‘yan bindiga a Arewa maso yamma, da rikicin kabilanci a Arewa ta tsakiya.

A yankin kudancin kasar nan ma akwai hare-hare kan hukumomi da jami’an tsaro da ake dangantawa da kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biyafara a kudu maso gabas, kazalika da kai hare-hare kan ‘yan Arewa a yankin kudu maso yamma da dai sauransu.


No comments