Yadda Taron Sallah, Hawan Bariki Da Hawan Daushe Zai Gudana A Masarautar Zazzau


Daga Nuhu Basheer Masa

A taron manema labarai da mai Martaba Sarkin Zazzau Amb. Ahmad Nuhu Bamalli ya kira kan sallar Idi, Sarkin Zazzau na 19 Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli a yayin zantawarsa da manema labarai ya bayyana tsarin yadda za a yi sallar idi da kuma bikin hawan Sallah kamar yadda al'ada ya tanadar har ya zuwa yanzu dai shirye-shirye ya kammallw na yin sallar idi a Masallacin filin Mallawa dake Kofar Doka a hanyar Jos bayan kwashe shekara 62 ba a yi sallar idi a wurin ba.

Kafin zuwa filin idin Mallawar dai mai Martaba Sarki zai bi ta Kofar "Bai" ne kamar yadda Mallawa ke yi bisa al'ada sai a fito ta Ban Zazzau daga nan bayan sallar tare da mai girma Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-rufai tare da sauran manyan baki, Hakimai, Dagatai da masu Unguwanni da sauran al'ummar Musulmi baki daya.

Bayan idar da sallar da gabatar da jawabi sai hawan ya fara daga hanyar Jos ya zuwa Kofar Doka, Zuwa Rimin Tsiwa, ya zuwa Babban Dodo sai a gangara Fadar ta mai Martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli daga nan sai jawabi tare da Gwamna  Nasir El-Rufai da manyan baki da sauran Hakimai.

Sai dai bana bayanin mai Martaban zai sha Bamban da sauran yadda aka saba don Sarkin akan Doki zai gudanar da bayanansa.

Sai rana ta biyu, ranar Hawan Bariki inda Hakimai za su fito da karfe 7:00 na safe shibkuma Mai Martabar zai fito da karfe 7:30 na safe inda za a tashi daga fadar mai Martaban ya zuwa hanyar Kofar Doka, Tudun Wada, PZ sai a shiga GRA zuwa filin Polo inda manyan baki irin su Gwamnan jihar Kaduna za su zauna domin jiran isowar mahayan, bayan isar Sarki da sauran Hakimai sai a yi jawabi sannan a kara dawowa a biyo hanyar da aka biyo har zuwa Babban Dodo sai a koma fada shima ayl yi jawabai sannan a tashi da karfe 12:00 na rana ya zuwa Masallacin Juma'a.

Sai rana ta uku; ranar Hawan Daushe za a yi gaisuwar Fada wanda Hakimai ke yi da safe karfe 10:00 na safe sannan Hawan Daushe za a yi kamar yadda aka saba a yashi daga Fadar ta Zazzau, Kaura, Kofar Gayan, Bakin Kasuwar Zaria, Babban Dodo zuwa Fada. 

Post a Comment

0 Comments