Yadda Wasu Ɓangarorin Ɗarika, Izala Da Shi'a Suka Yi Sallar Idi A Nijeriya A Yau LarabaMabiyan Ɗarikar Tijjaniya a Nijeriya sun yi Sallar Idi tun bayan da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya tabbatar da ganin watan Ramadan a garuruwan Bauchi da Azare. An yi Sallar ne a gidansa dake kan Titin Ƙofar Gombe dake cikin garin Bauchi. Ɗaruruwan Mabiyansa ne suka halarci Sallar. 

Sheikh Bashir Ɗahiru Usman Bauchi ne ke Gabatar Da Huɗubar Farko, Shehin Yana Magana kan Tabbacin Ganin Watan Shawwal da suka yi. 


Ya bayyana cewa; Muna da uzuri wajan Allah domin mun samu Nassi tabbatacce dake nuna idan an ga wata a Azumi 29 ya zama dede za'a yi Sallah. Ya ƙara da cewa; Amfani da Na'ura ba Matsala bace amma yana iya zama Matsalar daga ƙarshe idan Ilimin da ya samo ta ya kuma gano cewa tanada Matsala.

Ƴan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da Sallar Idi a garin Zariya. Wakilin ‘Yan uwa Almajiran Ibraheem Zakzaky na garin Zariya Sheik Abdulhameed Bello Zariya, shi ne ya Jagoranci Sallar wacce ta tare Jama'a sosai a yayin Sallar.

Tun a farko dai ya gabatar da Huɗuba da Nasihohi ga Mahalarta sallar, tare da addu'o'in zaman lafiya. Ƴan Shi'a sun bayyana tabbacin ganin wata a wata takardan Sanarwa da suka fitar jiya Misalin ƙarfe 9 da minti 57 na dare wacce Sheik Abdulhameed Bello ya sanyawa hannu akai.

Wannan wasu hotuna ne da Shafin Da'irar Zariya na Facebook ya wallafa sa safen nan yau Laraba. Mabiya Shi'ar sun yi Sallar a garin Bauchi, Potiskum da sauran garuruwa.


A garin Muradun Na Zamfara Wasu Mabiyan Ƙungiyar Izala sunyi Sallar Idi, bayan samun Tabbacin ganin Jaririn watan Shawwal, haka A Garin Dirin daji Sakaba Local Government a Jihar Kebbi suma yan Izalar Garin sun gudanar da Sallah a Yau.


-Rahoton Jaridar Walkiya 

Post a Comment

0 Comments