Yadda 'Yan Bindiga Suka Sace Daliban Islamiyyah Da Yawan Gaske A Jihar Neja

 


Hukumomi a jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya sun ce an saki dalibai 11 cikin kusan 150 da wasu 'yan bingida suka sace lokacin da suka kai hari kan wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina.

Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun sace gwamman dalibai makarantar Salihu Tanko Islamic School, koda yake sun saki wasu daga cikin daliban saboda kanana ne.

A cewar shaidun 'yan bindigar sun rika harbi kan mai-uwa-da-wabi kafin daga bisani su dauke daliban.

Sai dai cikin wata sanarwa da gwamantin jihar ta fitar ta ce an harbi mutum biyu lokacin harin kuma an tabbatar da mutuwar daya daga ciki, yayin da guda ke cikin mawuyacin hali.

Kazalika gwamnatin ta ce tana ci gaba da tattara bayanan tsaro kan harin, kafin daga bisani ta dauki matakan da suka dace.

Shugaban makarantar ya shaida wa BBC cewa akwai sama da dalibai 200 a cikin makarantar lokacin da yan bindigar suka shiga cikin harabar makarantar amma "adadin daliban makarantar shi ne 302."

"Ba za mu iya tantancewa kan [yawan] dalibai da aka sace a halin yanzu ba saboda wasu daga cikin daliban sun rika fita ta window suka kutsa suka gudu. Wasu kuma daga cikin daliban akwai kamar mutum 11 wadanda sun ga kananan yara ne 'yan shekaru biyar zuwa shida ba za su iya tafiya ba, sai suka sake su," in ji shugaban makarantar.

A cewarsa, daliban da aka sace sun hada da mata da maza sannan an hada da wasu malamansu yana mai karawa da cewa "ni ma da nake magana da kai akwai diyana biyu wadanda ni na haife su suna ciki duka an wuce da su; akwai kanwata uwa daua uba daya ita ma an wuce d ita."

Ya kara da cewa da misalin yammacin ranar Lahadi ne 'yan bindigar suka shiga garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar ta Neja.

"A babura suka isa wajen dauke da bindigogi, babu wanda ba a firgita ba a garin, tunda harbe-harbe kawai suke yi ta ko ina," a cewarsa.

Sace daliban makaranta a Najeriya na neman zama ruwan dare, ko a watan Fabirairu sai da aka sace É—aliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda 41 a Jihar.

Post a Comment

0 Comments