Yadda 'Yan Bindiga Suka Sake Kashe Mutum Biyu A Kaduna

 


Daga Muhammad Farouk 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutum biyu tare da raunata wasu maza shida a wasu hare-hare daban-daban da suka kai kananan hukumomin Chikun da Kajuru ta jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Kaduna.

Mista Aruwan ya ce jami'an tsaro sun ba da rahoton cewa 'yan bindiga sun mamaye Mazari, wani gari kusa da Buruku a karamar hukumar Chikun, mutum daya ya mutu a harin, sannan wasu uku sun jikkata.

Ya bayyana cewa a wani lamarin, yan fashin sun kai hari a kauyen Doka, karamar hukumar Kajuru, sun kashe mutum daya tare da raunata wasu uku.

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar 'yan bindiga a jihohin kasarnan. Kuma daruruwan mutane ne 'yan bindigar suka kashe ko suka yi garkuwa da su a cikin' ‘yan shekarun nan.

Sauran jihohin da irin wannan ta'addancin ya shafa sun hada da Neja, Zamfara da Katsina da Sakkwato.


Post a Comment

0 Comments