Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Ba Su Fi Karfinmu Ba, Inji Gwamnatin Tarayya

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa gwamnati na ƙoƙarin kawo ƙarshen mata...


Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa gwamnati na ƙoƙarin kawo ƙarshen matalar tsaro a ƙasar nan.

Ministan yace zargin da wasu mutane suke cewa gwamnati bata damu da ta magance waɗannan matsalolin ba bashi da tushe balle makama.

Ya ƙara da cewa ba da jimawa ba ‘yan Najeriya zasu ga sakamakon ƙoƙarin da gwamnati take na dawo da zaman lafiya a ƙasar nan, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a wani jawabi da yayi a jihar Lagos, yace:

"Ba wani sabon labari bane cewa Najeriya na fama da matsaloli kala daban-daban na tsaro, na karanta wasu magan-ganu dake cewa gwamnati tana rufa-rufa kuma bata da dabarun yadda zata magance matsalolin."

"Ina mai tabbatar wa yan Najeriya cewa yayin da gwamnati ta fahimci ƙalubalen tsaron da ake fama dashi; ta'addanci, yan bindiga, satar mutane, da rikicin manoma da makiyaya, gwamnati ba ta lulluɓe komai."

Kuma gwamnati ta tanadi duk abinda yakamata domin kawo ƙarshen matsalar kamar yadda zaku gani bada jimawa ba.

Muhammed ya ƙara da cewa gwamnati tasan maɓoyar masu satar mutane, ya ce hukumomin tsaro na bi a hankali ne saboda gudun haɗawa da fararen hula.

Yace: "Wuraren ɓoyon waɗannan masu satar mutanen ba abune boyayye a wajen jami'an tsaro ba, suna bi a hankali ne tare da kulawa domin gujewa cutar da mutanen da suka je kuɓutarwa."

"Jami'an tsaro suna da duk abinda ake buƙata domin magance ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama dashi."

Rahoton Legit

No comments