Daga Shafiu Umar
'Yan Bindigar da suka shiga garin Shadadi ta jihar Neja a satin da ya gabata, sun yi garkuwa da diyar wani mawaki kuma suka tilasta masa yin wake da zai yabe su sannan su saki diyarsa.
Wakilinmu ya labarto mana cewa; akwai yiwuwar mawakin ya shirya zai yi wakar kamar yadda suka umurta domin ganin ya kubutar da 'yar ta shi. Domin bayanai sun tabbatar da cewa; sun yi wa mawakin barazanar cewa idan bai yi musu waka ba zabsu kashe masa diyarsa.
Wakilinmu ya tabbatar mana da cewa; mawakin ya shirya shiga dakin yin waka a yau Litinin 10 ga watan Mayun 2021 domin yi musu wakar.
Wasu bayanai sun bayyana mana cewa; amshin wakar zai kasance kamar haka; 'IDAN KUN SHIGO GARI NA SHEDA BABU SAURAN MAZA KIDNAPAS'.
Jihar Neja dai na daya daga cikin jihohin Arewacin Nijeriya da ke fama da matsalolin rashi tsaro, inda a kwanakin baya gwamnan ya furta cewa fiye da kauyuka 50 a jihar na karkashin ikon 'yan bindiga da Boko Haram.
0 Comments