Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 15 A Jihar Neja

Daga Shafiu Umar Da sanyin safiyar yau Asabar 22 ga watan Mayun 2021 ne, wasu sansanin 'yan Bindiga suka dira wani gari da a...Daga Shafiu Umar

Da sanyin safiyar yau Asabar 22 ga watan Mayun 2021 ne, wasu sansanin 'yan Bindiga suka dira wani gari da ake cema Mangwaro a jihar Neja, inda zuwan su ke da wuya suka bude wuta. Sai dai wakilinmu ya shaida mana cewa an yi artabu sosai tsakanin 'yan bindigar da kuma mutanen garin.

Wakilin MADOGARA ya labarto cewa a halin yanzu an yi jana'izar mutum 15 yayin da wasu da a kai ga tantance adadinsu ba ke kwance a asibiti ana kokarin ceto rayukansu.

Sai dai wadansu bayanai da wakilanmu ya samu na nuni da cewa; suma mutanen garin sun yiwa 'yan bindigar barna sosai sai dai har yanzu ba a tantance ko nawa aka kashe ko raunatawa daga bangaren 'yan bindigar ba. 


No comments