‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Garin Gulbin Boka Ta Jihar Neja


Daga Sani Muhammad Sani Gulbin Boka

Da ranar yau Lahadi 2 ga watan Mayun 2021 da ‘yan bindiga suka kai hare-haren ta'addanci a garin Gulbin Boka dake karamar hukumar Mariga da wasu kauyukan dake kusa da garin. ‘Yan Bindigar sun shiga wani gari da ake kira Kampani dake kusa da wani gari da ake kira Warari, inda suka kwashe duk shanun dake garin kama yadda majiyarmu ta tabbatar.

Bayanai sun nuna cewa; bayan ‘yan bindigar sun koro shanun da suka sato sai suka biyo ta Gulbin Boka domin kwasar wasu shanun, wanda dama yau ne Kasuwar Garin Gulbin ke ci wanda hakan ya sa suka yi karya karar da ake daure shanun a kasuwar suka kora wasu kamar yadda wakilin MADOGARA ya labarta.

Wakilinmu har wala yau ya shaida mana  cewa; a lokacin shigowar Barayin Shanun sun bude wuta har suka harbi mutum daya wanda ake kira Abdullahi.

Wakilinmu ya tabbatar mana cewa; an wuce da wanda aka harba asibitin Kontagora domin ceto rayuwarsa, sai dai har ya zuwa hada wannan rahoton ba mu samu labarin ‘yan bindigar sun yi garkuwa da kowa ba.

Shigowar ‘yan bindigar Gulbin Boka har tsakiyar kasuwa kuma suka zarce Karar Shanu kai tsaye ya tayar wa mazauna garin hankali sosai, ta yadda suka ga rundunar ‘yan bindigar ba adadi sun doso ba fargaba har suka yi abin da za su yi suka fita lafiya ba tare da wani mataki daga jami'an tsaro ba.

Idan ba ku manta ba, gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello tuni ya shelanta cewa mayakan Boko Haram sun mamaye kauyuka fiye da hamsin a jihar, inda harma sun kafa tutarsu a wata karamar hukuma. 


Post a Comment

0 Comments