'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamishina A Jihar Kogi


Daga Wakilinmu

Wadansu 'yan bindiga a ranar Asabar sun kashe Kwamishina a yayin da yake tafiya a jihar Kogi kamar yadda 'yan sanda suka tabbatar. 

Solomon Adebayo, Kwamishinan Fensho na jihar Kogi an kashe shi ne a Kabba dake Ilorin da yammacin ranar Asabar. 

Kakakin 'yan sandan jihar Kogi, William Ayah, ya ce 'yan bindigar sun budewa motar Solomon Adebayo ne wuta ne inda suka kashe shi nan take. Suka kuma jikkata direbansa. 

'Yan sandan sun ce za su kaddamar da bincike domin kamo wadanda suka aikata hakan.

'Yan sandan sun ce babu tabbacin ko 'yan Bindigar sun yi awon gaba da wani abu na Kwamishinan. 

Post a Comment

0 Comments