Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan bindiga Sun Kashe Sojojin Sudan Ta Kudu Guda Huɗu

Dakarun sojan Sudan ta Kudu huɗu ne aka tabbatar sun mutu bayan wasu 'yan bindiga sun buɗe wa motarsu wuta a kan titin Yei d...


Dakarun sojan Sudan ta Kudu huɗu ne aka tabbatar sun mutu bayan wasu 'yan bindiga sun buɗe wa motarsu wuta a kan titin Yei da ke Juba, babban birnin ƙasar.

"Da ganin yadda lamarin ya faru, hari ne da aka tsara shi domin a hari jami'an gwamnati," a cewar ƙaramin ministan yaɗa labarai, Paulino Lukudu Obede yayin hirarsa da BBC.

"An yi wa motar ministan kananan hukumomi ruwan harsasai ita ma," in ji shi.

Ya zuwa yanzu babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin.

Ministan Ƙananan Hukumomi Moro IsaacGenesio ba ya cikin motar tasa a lokacin harin na ranar Alhamis.

No comments