Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yan Sandan Zamfara Sun Kama 'Yan Bindiga Biyar Harda Dan kasar Waje

'Yan sanda a Jihar Zamfara sun tabbatar da cewa sun kama mutum biyar da ake zargi da aikata fashi da garkuwa da mutane da ku...


'Yan sanda a Jihar Zamfara sun tabbatar da cewa sun kama mutum biyar da ake zargi da aikata fashi da garkuwa da mutane da kuma mallakar makamai ba bisa a'ida ba.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a jihar, Shehu Mohammed, shi ne ya bayyana su ga manema labarai a jiya Juma'a a hedikwatar rundunar da ke Gusau babban birnin jihar.

Daga cikin mutanen har da wani da aka bayyana a matsayin ɗan ƙasar waje. Mutumin ya ce ya sayar wa da 'yan fashi bindiga aƙalla 450.

Ya ce an yi nasarar kama su ne sakamakon haɗin gwiwa da suka yi da ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah rashen jihar ta Zamfara.

Waɗanda aka kama ɗin, rahotanni sun bayyana cewa su ne ke addabar garuruwa da dama a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina, inda suke kashe mutane tare da kama wasu don karɓar kudin fansa.

Shehu ya ce rundunar za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran ƙungiyoyin da ke da niyyar ba su gudummawa wajen inganta tsaro a jihar.

No comments