YANKARA: Mahara Kullum Na Cin Kare Su Ba BabbakaDaga Yankara Abu Ɗaheera

Tuni na daukarwa kaina daina magana kan halin da mahaifata (Yankara) take ciki, musamman saboda yadda nake saka al'umma cikin tunani da firgici. Amma a wannan lokacin abin sai ya zo da ban tsoro.

Tun daga ranar Asabar 1/5/2021 har zuwa yau 7/5/2021 Allah ke da kullum, amma kullum sai waɗanda ake kira mahara sun shigo garin Yankara sun ɗauki mutane. Bayan sun ɗauka za su saki harsasai kamar zubar ruwa, wani lokaci ma har su rinƙa zuga kansu da kalmomi na kirari.

Abin ban haushi shekaran jiya ma har da kiran salla suka yi kafin fara ta'addancin, bayan sun ɗauka kuma suka yi kabbarori sannan suka yi ihu suna cewa ina mazajen suke, kafin daga bisani su buɗe wutar da ta hana mu raya daren Lailatul Qadr.

Kar a manta, cikin garin na YANKARA akwai wasu GAWARWAKI da ake kira SOJOJI masu samar da tsaro a garin. Sojoji ne danƙam fiye da lissafi, wadanda ba za ka iya yin tafiya ta minti guda cikakke ba tare da ka haɗu da SOJA a garin ba.

Da rana sun gwanance wajen hawa motoci da zagayen garin, idan ka gitta masu su yi maka shegen wulakanci. Idan ma ka je sansaninsu da abin hawa dole sai ka sauka ka tura, in ma buɗaɗiyar mota ce duk mutanen ciki sai sun sauka.

Duk da irin wannan yawa na SOJOJI haka 'yan ta'addan ke shigowa garin Yankara su ci karen su babu babbaka su ƙara gaba. Sai sun tafi, sannan su biyo baya da harba tasu bindigar suna burgagin banza.

Daga shekarar da ta gabata, zuwa yau zan iya tabbatar da cewa a Yankara kawai, an dauki mutane sun fi dubu waɗanda sai da aka biya kuɗin fansa, wasu kuma an kashe su har lahira. Amma gwamnatin Jihar ba jaje ba ta'aziyya ba sannu ba an gaishe ku. Kullum zararmu ake yi kamar karan danni, sai dai idan an kawo hari dare na yi a mayar da mu gida a garƙame ba ka da damar fitowa tun 9 har sai 6.

To, jiya ma dai sun shigo tun kusan ƙarfe 12:30 suke harba bindigu har kusan 1:20 kuma sun kwashi 'yan mata tare da matan aure sun tafi da su.

Abu Daheerat ya rubuto ne daga garin Yankara dake karamar Hukumar Faskari ta jihar Katsina. 

Post a Comment

0 Comments