YANZU-YANZU: Buhari Ya Cire Hadiza Bala Ya Nada Koko A Matsayin shugaban NPA


Daga Muhammad Farouk

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cire Hadiza Bala Usman a mukaminta na shugabar Hukumar NPA kamar yadda majiyarmu ta Jaridar People's Gazette ta labarto. 

Shugaban ya nada Mohammed Koko ya maye gurbin Hadiza Bala Usman.

Kafin nadin Mohammed Koko shi ne Daraktan kudi na Hukumar. 

Majiyarmu ta tabbatar da cewa Hadiza Bala Usman ta tabbatar musu da cire ta daga mukaminta da aka yi. Amma ba a sanar da ita hukumance ba daga ma'aikatar zirga-zirga. 

Sai dai Kakakin ma'aikatar zirga-zirgar bai biyo sakon da majiyarmu ta aika masa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya nada Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar NPA a 2016, wanda daga hawanta ta fara kawo sauye-sauye da ya taimakawa Hukumar ta zama daya daga cikin Hukumar da ke tattara haraji ga gwamnatin Nijeriya. 

Post a Comment

0 Comments