Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: Buhari Ya Nada Manjo Farouk A Matsayin Sabon Shugaban Sojoji

Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya. Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar d...


Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya.

Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis.

Naɗin na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar.

Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku.

Tun bayan rasuwar Manjo Attahiru ƴan Najeriya suka fara tsokaci kan waɗanda ake hasashen za su maye gurbinsa.

Kafin naɗin nasa, Manjo Janar Faruk Yahaya shi ke jagorantar yaƙi da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko.

Rahoton BBC Hausa

No comments