YANZU-YANZU: Daga Zuwa Neman Aiki Ya Yi Mata Fyade Ya Kashe Ta

 

Iniubong Umoren

Daga Muhammad Haruna

An tsinci gawar wata matashiyar budurwa mai suna Iniubong Umoren, wanda yake daliba ce da ta karanci ilimin Falsafa a Jami’ar Uyo dake jihar Akwa Ibom MADOGARA ta labarto.

Majiyarmu ta FIJ ta labarto cewa; wata makusanciyar matashiyar, Umoh Uduak, ita ce ta tabbatar da labarin a ranar Lahadi a wani sakon bidiyo da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda take kuka ta bayyana cewa; “sun yi kawata fyade sun kuma kashe ta”, ta tabbatar.

Kawar ta ta ta tabbatar da cewa sai da aka yi wa Iniubong fyade sannan aka kashe ta.

Shafukan sada zumunta ya cika da maganganu iri-iri tun ranar 29 ga watan Afrilun 2021, a lokacin da Umoh ta aika da wani sakon gaggawa na neman taimako, inda ta yi zargin an yi garkuwa da kawarta bayan da ta amince ta halarci wani jarabawar neman aiki a wajen Akwa Ibom.

Umoh ta rubuta cewa; “ta shaida min cewa za ta je jarabawar neman aiki a airport road, wanda yake yana da nisa da gidansu. Jim kadan, sai ta aika min da sakon murya na dakika daya a WhatsApp, sai na kira ta domin na ji ko tana son ta ce min wani abu ne, amma ina kiranta na fara jin ihu”, ta labarta.

Hakan ya sanya Umoh ta rubuta a shafinta na Twitter tana neman a taimakawa kawarta saboda ita a cewarta tana Legas; “kawarku na bukatar taimakon mu. Ni ina Legas ne ba zan iya taimakonta ba da ya wuce na wallafa sakon nan”, ta tabbatar.

Hakan ya sanya ‘yan Nijeriya da dama a shafin na Twitter suka kaddamar da kamfen da HashTag na #FindHinyUmoren, domin binciko wannan matashiryar budurwar, inda daga bisani ‘yan sanda suka cafke mutum biyu da ake zargi a bacewarta.

Kwanaki biyu kafin bacewar Iniubong ta wallafa tana neman aiki a shafinta na Twitter, inda ta rubuta cewa; “ku taimaka ina matukar bukatar aiki, wani abu da zan rika yi da zai taimakawa jikina da ruhina a yayin da nake bada gudummawata ga kamfanin”, ta rubuta.

Ta ci gaba da cewa; “ina zaune ne a Uyo, ina da fasaha, ina da kwazon wajen zurfin tunani, abu mafi muhimmanci ina da saurin fahimtar abu. Idan an bukaci na tura CV dina zan yi hakan”, ta wallafa cikin harshen Turanci a ranar 27 ga watan Afrilun 2021.

 

Post a Comment

0 Comments