Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: El-Rufai Na Neman Shugaban NLC Ayuba Wabba Ruwa A Jallo, Ya Sa Farashi Ga Duk Wanda Ya Kamo Shi

Daga Ammar Muhammad  Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya ayyana shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Ayuba Wabba a...

Daga Ammar Muhammad 

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya ayyana shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Ayuba Wabba a matsayin wanda yake nema ruwa a jallo bisa zarginsa da yunkurin durkusar da tattalin arzikin jihar sakamakon sanya ma'aikata su tafi yajin aiki har na tsawon kwana biyar a fadin jihar. 

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa da safen yau Talata a shafinsa na Twitter wanda wakilin MADOGARA ya bibiya, inda ya sanar cewa; "Ayuba Wabba da sauran 'yan kungiyar kwadago ta kasa (NLC) na ayyana su a matsayin waɗanda nake nema ruwa a jallo bisa durkusar da tattalin arziki da hari kan kayayyakin gwamnati a karkashin dokar 'Miscellaneous Offences Act'. Duk wanda ya san inda ya boye ya aika wa ma'aikatar shari'a ta jihar Kaduna sako, akwai sakamako mai tsoka", ya tabbatar. 

Al'umma dai na ci gaba da zura ido domin su ga yadda za ta kaya tsakanin gwamma Nasir El-Rufai da kuma kungiyar kwadago ta kasa bisa yajin aikin gargadi na kwana biyar da NLC din suka ayyana a jihar, wanda gwamnan ya ce hakan ba zai sanya ya sauya matsaya ba kan korar ma'aikatan. 

No comments