Fasto Rabaran Ejike Mbaka ya bayyana a garin Enugu bayan mabiyansa a yau Laraba sun cika tituna suna zanga-zangar zargin jami'an tsaro da hannu a bacewarsa.
Rahotannin da suka shigo mana daga Jaridar The Nation na nuni da cewa Fasto din ya bayyana. Inda mabiyansa suka cika da murna.
Bayanai sun nuna cewa; Fasto din ya bayyana ne sanye da shudin kaua yana dagawa dandazon mabiyansa hannu cikin annashuwa.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter an rika jin iface-iface akan ababen hawansu suna cewa; "Mbaka ya dawo" cikin harshen Igbo.
0 Comments