YANZU-YANZU: Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Dokar Kulle Da Hana TarukaGwamnatin Tarayya a yau Litinin ta ayyana dokar hana zirga-zirga a duk fadin kasar sakamakon dawowar annobar cutar Korona. Inda ta ce ta hana zirga-zirgar daga karfe 12 na dare zuwa 4 na Asuba. 

Dokar hana zirga-zirgar wanda Mukhtar Mohammed ya sanar a taron manema labarai da Kwamitin dakile annobar cutar korona ta shugaban kasa ta kira a birnin Tarayya Abuja, ta ce dokar zai fara aiki ne daga ranar Litinin 10 ga watan Mayu din 2021. 

Kwamitin har wala yau ya haramta bude wuraren shakatawa, wuraren motsa jiki tare da haramta tarukan addini wanda suka ce ka da mutane su wuce mutum 50 a kowanne taron addini. 

Sannan sun umurci da a rika bada tazara a yayin tarukan. 

Post a Comment

0 Comments