YANZU-YANZU: Gwamnatin Tarayya Ta Zargi Shugabannin Siyasa Da Yunkurin Yi Wa Buhari Juyin Mulki


Daga Muhammad Farouk

Gwamnatin Najeriya ta zargi wasu da kokarin ingiza sojoji su kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. 

Wannan labarin ya fito ne bayan taron majalisar tsaron kasa da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja. 

Da fari dai sojojin kasar sun yi gargadi a kan duk wani yunkuri mai kama da wannan, suna mai cewa ba za su yi hakan ba. 

Fadar shugaban kasar har wala yau ta ankarar da 'yan Nijeriya kan zargin yunkurin juyin mulki daga wasu shugabannin addini da na siyasa da suke son yi wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. 

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina shi ne ya yi wannan gargadin a sanarwar da ya fitar a ranar Talata, inda ya alakanta zargin na sa da gargadin da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta yi. 

Sanarwar ta ce fadar shugaban kasar ta lura da yadda wasu kungiyoyi da daidaikun mutane ke rura wutar rikici a kwanakin nan da nufin haifar da yanayin da zai sanya a fitar da rai ga shugaba Buhari. 

Inda ta ce ba za ta zura ido hakan ya auku ba, za ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin hada kan kasar har zuwa lokacin da wa'adin mulkinsu zai kare a 2023 ba tare da damuwa da me za a ce ba.  Post a Comment

0 Comments