Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC a karkashin jagorancin Ayuba Wabba ta amince da tayin gwamnatin Tarayya na sulhu tsakaninta da gwa...
Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC a karkashin jagorancin Ayuba Wabba ta amince da tayin gwamnatin Tarayya na sulhu tsakaninta da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a daren nan a taron manema labarai da suka kira a Kaduna.
Da yammacin yau Laraba ne gwamnatin Tarayya a karkashin ministan Kwadago Chris Ngige ya aikawa Gwamna Nasiru El-Rufai da shugabannin kungiyar kwadago takardar sasanta su.
Cikakken rahoto na nan tafe.
No comments