Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: Kungiyar Kwadago Ta Garkame Makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic Ta Zariya

Daga Ammar Muhammad Labarin dake shigowa MADOGARA da safen nan na nuni da cewa; kungiyar kwadago (NLC) ta je makarantar kimiyya...


Daga Ammar Muhammad

Labarin dake shigowa MADOGARA da safen nan na nuni da cewa; kungiyar kwadago (NLC) ta je makarantar kimiyyah da fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic dake Zariya wacce take hanyar Kaduna, inda suka kori dalibai da Malamai, sannan suka kulle makarantar, suka kuma tafi da makullin.

Hakan ya biyo bayan kin bin umurnin NLC din da ma'aikatan makarantar suka yi na kin zuwa yajin aiki sakamakon korar ma'aikata da kin biyansu hakkokinsu da gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai ke yi wanda hakan ya sabbaba NLC tsunduma yajin aikin gargadi na kwana biyar. 

A jiya Litinin ne dai NLC ta shiga yajin aikin a fadin jihar Kaduna, inda MADOGARA ta labarto cewa; a Zariya kawai, yajin aikin na kungiyar kwadago ya shafi dukkanin Bankuna, gidajen Man Fetur, wutar lantarki da kuma ma'aikatun gwamnati. 

Wakilin namu wanda ya zagaya kananan hukumomin Zariya da Sabon Gari a jiya Litinin ya tabbatar mana da cewa; babu wutar lantarki tun jiya da yamma har ya zuwa yau Talata. A yayin da bankuna kuma suka kasance a rufe. 

Su kuma gidajen Man Fetur kuwa ana zuba dogon layi a cikinsa saboda fargabar karancin mai din sakamakon hana shigowar Motocin jigilar man fetur din zuwa Kaduna. A yayin da waɗansu gidajen man fetur din suke a garkame. 

Suma ma'aikatan gwamnati sun ki zuwa wurin aiki sakamakon umurnin na NLC. Sai dai wasu ma'aikatan kamar na Nuhu Bamalli Polytechnic sun bijirewa umurnin NLC, wanda hakan ya sanya NLC din a yau Talata suka dira makarantar suka kulle ta. 

No comments