YANZU-YANZU: Masallata Sun Kwashe Fiye Da Awa Biyu Ana Jiran Sarkin Zazzau Ya Bayyana A Yi Sallar Idi


Daga Wakilinmu

Bayan sama da shekara 62 ba a yi sallar Idi a filin Mallawa dake Kofar Doka Zariya ta jihar Kaduna dake sabon titin Jos ba, a yau Alhamis ne al'umma su taru domin gabatar da sallar Idi a Filin na Mallawa inda dubun-dubatar mutane suka samu damar halarta. Sai dai al'umma da dama sun nuna takaicinsu na yadda suka kwashe sama da awa biyu suna jiran isowar Sabon Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli da kuma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai domin gudanar da sallar. Wanda wasu suka isa muhallin sallar tun karfe 8 na safe, amma har ya zuwa karfe 9:46 na safen, Sarkin da tawagarsa ba su iso ba balle a tada sallar. 

Wakilin MADOGARA TV da ya je muhallin da za a yi sallar ya shaida mana cewa da yawa sun gaji da jira ma har sun fara tafiya ba tare da sun yi sallar ba, don kuwa sun saba duk shekara karfe 9 ake fara sallar, amma sai ga shi yau har karfe goma saura sabon Sarki bai zo ba haka gwamna ma bai zo ba balle a tada sallar.

Post a Comment

0 Comments