YANZU-YANZU: Minista Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan YuniSheikh Isa Pantami, ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani ya ce an kara wa'adin hade layukan SIM da lambar shedar dan kasa  wato NIN.

An tsawaita wa'adin shirin har zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2021. 

Jaridar Punch ta labarto cewa bayanin hakan na cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadin gwiwar Daraktan hulda da jama’a na hukumar sadarwa ta Nijeriya, Ikechukwu Adinde; da kuma Shugaban Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa, NIMC, Kayode Adegoke. 

An kuma tattaro cewa Pantami, wanda ya sha suka kan kalamansa na baya kan kungiyar Taliban, ya bayyana cewa an hada katunan SIM miliyan 54 da NIN. 

A wani labarin, mun ji a baya cewa Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba sakamakon ci gaba da alakanta lambobin shedar kasa (NINs) da katinan SIM. 

Daily Trust ta ruwaito cewa NCC a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 6 ga Janairu, ta ce bayanin ya zama dole don kawar da tsoron masu amfani da layuka da sauran jama’a.  

An ruwaito mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Adinde yana cewa wani binciken da aka gudanar kwanan nan akwai kusan katinan SIM guda hudu zuwa biyar ga kowane dan Nijeriya mai amfani da waya. 

Post a Comment

0 Comments