YANZU-YANZU: An Sake Yi Wa Buhari Basillar Rigakafin Korona


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake karɓar allurar rigakafin korona ta AstraZeneca a karo na biyu.

Fadar shugaba kasa ce ta wallafa hotunan a shafin Twitter, inda hotunan ya nuna lokacin da yake karbar rigakafin a ranar Asabar.

Tun a farkon watan Maris shugaban ya karbi allurar ta farko, kuma yanzu ya kammala karɓar rigakafin ta korona.

Post a Comment

0 Comments