Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Saad Abubakar Na III ya ce ba a ga watan Sallah ba a fadin Nijeriya don haka idi sai ranar Alhamis.
MADOGARA ta labarto cewa; mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa a dubawar da aka yi a yau Talata ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Nijeriya.
Ya ce don haka ranar Alhamis 13 ga watan Mayu ne za a yi sallar idi ta karamar sallah a Nijeriya.
0 Comments