Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: Shugaba Buhari Zai Shiga Tsakanin El-Rufai Da Kungiyar Kwadago

Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baiwa Ministan kwadago da ayyuka na kasa Sanata Chris Ngige umurni ya gaggauta shiga...


Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baiwa Ministan kwadago da ayyuka na kasa Sanata Chris Ngige umurni ya gaggauta shiga tsakanin Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da Gwamnatin jihar Kaduna domin kawo karshen yajin aikin dake faruwa a Jihar. 

MADOGARA ta labarto cewa tuni ministan ya turawa Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El Rufai da manyan mukarrabansa da kuma shugaban kungiyar kwadago, Kwamared Ayuba Wabba da jagororin kungiyar ta NLC takardar gayyata zuwa ofishinsa a gobe Alhamis domin sulhu. 

Ministan ya ce za a yi zaman tattaunawar ce a ofishinsa dake Sakatariyar Gwamnatin tarayya a Abuja da karfe 11 na safe.

Dokar kwadago ta Trade Disputes Act, CAP . T8, Laws of  Federation of Nigeria (LFN) 2004; ta baiwa Ministan dama ya jagoranci duk wata tattaunawa domin kawo sulhu a duk wata baraka da ta shafi kwadago ko maikata a Nijeriya.

No comments