Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: 'Yan Jagaliya Sun Nemi Tarwatsa Zanga-zangar Kungiyar Kwadago A Kaduna

Daga Muhammad Haruna A ci gaba da bibiyar zanga-zangar kungiyar kwadago da MADOGARA ke yi, wakilinmu ya labarto mana cewa; wad...


Daga Muhammad Haruna

A ci gaba da bibiyar zanga-zangar kungiyar kwadago da MADOGARA ke yi, wakilinmu ya labarto mana cewa; wadansu 'yan jagaliyar siyasa sun nemi su tarwatsa masu zanga-zangar a yau Talata. Inda suka rika jifan masu zanga-zangar da duwatsu.

Masu zanga-zangar dai sun taru ne a Roundabout na NEPA dake tsakiyar garin Kaduna domin ci gaba da zanga-zangar da suka fara a jiya Litinin, suna tsaka da zanga-zangar sai ga 'yan jagaliyar sun iso wurin masu zanga-zangar suka fara jifa da duwatsu da kuma daddaga miyagun makamai.

Harin na 'yan jagaliyar ya sanya wadansu masu zanga-zangar sun buya domin tsira da rayukansu.

Sai dai har ya zuwa hada wannan rahoton babu tabbacin wadanda ya turo 'yan jagaliyar, sai dai shugaban kungiyar kwadago (NLC), Ayuba Wabba ya zargi gwamna Nasir El-Rufai da turo 'yan jagaliyar domin su tarwatsa su.

Da yake tattaunawa da gidan Talabijin na Channels Television ana tsaka da zanga-zangar, Wabba ya ce ya sanar da hukumar DSS bayan ya samu labarin yunkurin kawo wa zanga-zangar su hari.

"Yau rana ce ta bakin ciki a tarihin dimokuradiyyar Nijeriya. Da safiyar yau, muka samu sahihin labari cewa El-Rufai ya dauko hayar wani mai suna Alhaji Hassan da wadansu 'yan jagaliya domin su zo su kawo mana hari", inji shi.

Wabba ya ci gaba da cewa; "a lokacin da muke a nan, sai kuwa ga shi sun zo, amma cikin ikon Allah muka kora su saboda muna da yawa a nan. Mu ba 'yan jagaliya bane kuma ba za mu yi amfani da 'yan jagaliya ba saboda mu ma'aikatan gwamnati ne", ya tabbatarwa da Channels Television.

Sai dai 'yan jagaliyar ba su yi nasara tarwatsa masu zanga-zangar ba, domin jami'an tsaro sun antaya musu tiya gas suka watsa su.

Wabba dai a yau Talata yana Jagorantar zanga-zangar NLC a rana ta biyu duk da ayyana nemansa ruwa a jallo da gwamnatin Kaduna ta yi. 


No comments