Za Mu Ci Gaba Da Biyan Mafi Karancin Albashi Na Dubu Talatin -Gwamna Tambuwal


Daga Muhammad Farouk

Gwamnatin jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce ba zai gaza ba wajen ci gaba da biyan mafi karancin albashi na naira dubu talatin (30, 000) kamar yadda aka fara a shekarar da ta gabata, MADOGARA ta labarto. 

Hakan ya fito ne a sanarwar da Daraktan ofishin watsa labarai na mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdullahi Abubakar ya fitar. 

Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar ma'aikata ta 2021 a Sakkwato a ranar Asabar kamar yadda sanarwar ta tabbatar, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa tana gaba-gaba wajen biyan albashin ma'aikata tunda ya zama gwamnan jihar. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa; gwamnan ya tabbatar da hakan ne ta bakin mataimakinsa, Manir Muhammad Iya. Inda ya ce; "muna farko a jihohi wajen biyan albashi da fensho. Sannan muna kan gaba wajen tabbatar da fara biyan sabon tsarin mafi karancin albashi na naira dubu 30", ya tabbatar. 

Post a Comment

0 Comments