Wasu al'ummomi a Nijeriya daga bangarori daban-daban na ta shirye-shiryen gabatar da kudurorinsu a game da shirin kawo gyara ga kund...
Wasu
al'ummomi a Nijeriya daga bangarori daban-daban na ta shirye-shiryen gabatar da
kudurorinsu a game da shirin kawo gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.
Bbc
Hausa ta labarto cewa; a jihar Kaduna, maganar ta yi nisa wasu daga cikin
al'ummomin kudancin jihar na nuna neman a ba su na su bangaren a yayin da wasu
daga cikin yan kudancin ke cewa har yanzu ba su da cancantar a ce sun balle
daga Kaduna.
Jonathan
Osake shugaban kungiyar ‘yan kudancin Kaduna wato SOKAPU ya yi wa BBC karin
bayani game da hujarsu:
"Kudancin
Kaduna da bangaren arewacinsa an dade ana rashin zaman lafiya. Al'adunmu daban,
kuma mun san cewa idan aka raba jihar, kowa yaje yana cin gashin kansa, gaskiya
zai kawo zaman lafiya."
Sai
dai an gamu kuma an rabu. Kungiyar Fulani makiyyaya ta Mi Yati Allah da ita ma
ke cikin yankin na kudancin Kaduna ta ce ba da yawunta ba a cikin wannan
lamari.
Ibrahim
Bayero shi ne mai magana da yawun kungiyar ta Mi Yetti Allah:
"Abin
da su ka rubuta mu ba ma tare da su. A matsayinmu na Fulanin Kudanci, ba su
neme mu ba, saboda haka jihar Gurara da su ke nema, mu ba mu goyi bayan haka
ba. Idan za a kirkiro jiha sai an dubi tattalin arzikin yankin, al'ummar nan da
su ka rubuta wannan takardardun, gaba dayansu ba sa iya tara haraji."
No comments