Matasa daga sassa daban daban na Najeriya sun gudanar da
gangamin karbar mulki daga hannun dattawa.
Yayin da shekara ta 2023 ke kara
karatowa, matasa sun dage, inda suka ce suna da lakanin magance matsalolin da
kasar ke fuskanta har in sun sami madafun mulki daga hannun wadanda suka ci
zamaninsu dana ‘ya’yansu suke kuma cin na jikokinsu.
A hirar su da Muryar Amurka
matasan sun bayyana cewa, a shirye suke su kwace mulki a hannun wadannan
tsofafin. Bisa ga cewar su, duk cigaban da aka samu a Najeriya, matasa ne suka
cimma. Ko a lokacin Buhari da tsohon shugaba Yakubu Gowon da ya hada kan
Najeriya kuma ya ja yakin basasa, duk suna cikin kuriciyarsu ne a lokacin.
A nasu bangaren, matan da Muryar
Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa, zasu goya wa ‘ya’yansu baya don ba
matasan damar samad da dama ga mata da matasan Najeriya.
Aishatu Idris Yahuza daya daga
cikin matan da Muryar Amurka ta yi hira da su, ta ce dukkan Najeriya daya ne
amma matsalolin wariya ya kawo tashe-tashen hankali, shi ya sa ta ke mara wa
matasa baya su karbi mulki da karfinsu don a sami cigaba.
A bangare guda kuwa, Hajiya Hauwa
Lori da tayi kusan shekaru arba'in ana damawa da ita a harkokin siyasan
Najeriya ta ce shawarwarin manya nada muhimmanci.
0 Comments