Zunuban Hadiza Bala 12 Da Ya Sanya Buhari Ya Dakatar Da Ita Daga Shugabancin NPA


Daga Muhammad Haruna 

A ranar 25 ga watan Janairun 2021, Mujallar ‘Shipping World Magazine’ ta wallafa wadansu zarge-zarge da ake yi wa shugabar hukumar tasoshin ruwa ta Nijeriya, NPA, Hadiza Bala Usman tun tana kan mukaminta kafin daga bisani shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da ita tare da sanya a binciketa bisa dukkanin zarge-zargen da ake yi mata.

A wancan lokacin Mujallar ta wallafa cewa duk da wadannan zarge-zargenda ake yi mata, amma da yiwuwar ta kwashe shekara goma a matsayin shugabar hukumar. 

Jaridar MADOGARA ta fassaro cewa; daga cikin zarge-zargenda ake yi mata sun hada da; 

ZARGIN RASHAWA

1. Rushe kwangilar jigilar kaya tare da bai wa kanta da masu taimaka mata har na tsawon shekara goma (10). 

2. Shirin ‘Corporate Social Responsibility (CSR)’ da ya kamata ya zama tallafi ga al’umma wanda ake samu daga ayyukan tasoshin ruwan, amma sai ta maishe da shi kamar wani muhalli na kwasar kayan tana rabarwa babu lura musamman a yankin Arewa. 

3. kayayyakin da aka ware domin a taimakawa ‘yan gudun hijira amma sai ta maishe da shi kayan bayar da kwangila ta hanyar wuce gona da iri. 

4. PBT sun amince da a siyo motar Bas ga ma’aikata kirar Toyota Coaster amma sai aka siyo motar Bas ta ‘yan Chana. Haka zalika haka aka yi a batun siyo motocin daukar marasa lafiya (Ambulances).

5. Mafi yawan kwangilolin da ake bayarwa a NPA ana zargin tana bai wa wani dan uwanta ne (an sakaya sunansa) ta hanyar wadansu kamfanuka da aka kirkira da wadansu hanyoyin na daban. 

6. Sannan har wala yau tana yiwa dokokin bayar da kwangila da siyan kayayyakinda kuma farashin kayayyaki hawan kawara.

7. Akwai kwangila da ta bayar a kwanakin nan na siyo tocila guda 200 akan naira miliyan takwas. 

RASHIN IYA SHUGABANCI

8. Tana daukar wadanda suke hidimar kasa a NPA aiki wanda hakan ya sabawa ka’ida da dokokin da aka shimfida. 

9. Ta dauki sabbin daliban da suka kammala jami’a aiki kuma tana kara musu matsayi da mataki daya ko biyu cikin shekara biyu wanda hakan ya sabawa dokokin tafiyar da NPA da kuma dokokin aikin gwamnati. 

10. Tana yaudarar kwamitin lura da hukumar ta hanyar sanya su su sa hannu a wadansu karin mukamai ga wadansu zababbun jami’ai birbishin manyansu ta hanyar da bai dace ba wanda ya sabawa dokokin gwamnatin Tarayya na karin mukami a takarda mai lamba FC.6243/S.1/Vol.XV111/5 na ranar 28 ga watan Mayun, 2010, da kuma dokar da fadar shugaban kasa ta bayar a cvikin wata takarda mai lamba PRES/30-1 mai dauke da kwanan wata na 20  ga Satumban, 2004.

Kamar yadda aka jaddada a wannan takardar da aka rarraba mai lamba FCSC/CHMN/CL/17/Vol.1/36 na ranar 22 ga Oktoban, 2013 har yanzu dokar na aiki har ya zuwa yau; 

11. Yaudarar kwamitin lura da hukumar NPA wajen amincewa da sake rike jami’an da suka yi ritaya bisa kwangilar da ake dauke su ba tare da sun cika dukkanin wata ka’ida na sake ba su wannan dama ba bisa wadansu sharudda a karkashin dokokin karin wa’adin aiki. 

NUNA IKO DA ISA

12. Masu binciken kudi ana sauya musu aiki nan take da zarar sun bijiro mata da wadansu tambayoyin dangane da yadda aka yi wadansu harkallar, ko kuma yadda ‘yan kwangila suka siyo wadansu kayan musamman kan adadin kayan, nagartar kayan domin dacewa da dokoki da sharuddan da aka gindaya a takardar yarjejeniyar kwangilar da PBT ta amince. 

-Jaridar MADOGARA ce ta fassara rahoton.Post a Comment

0 Comments