A Maimaikon Kashe 'Yan Ta'adda Jiragen Yakin Nijeriya Sun Kashe Shanu Dubu Daya


Jiragen yakin sojin Nijeriya sun kashe shahu dubu 1 a wasu hare-hare da suka kaddamar kan Fulani a kananan Hukumomin Keana da Doma da ke jihar Nasarawa.

Shugabannin Fulanin yankin da wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa, sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, an kai farmakin ne  tsakanin 10 zuwa 13 ga watan Yuni da muke ciki.

Wasu matasan Fulani makiyaya sun samu  rauni, sannan sama da shanunsu 500 sun kwarara cikin jihar Benue mai makwabtaka da Nasarawa kuma har yanzu babu duriyarsu.

Rahotanni na cewa, an shafe tsawon sa’o’i uku ana kaddamar da farmakin a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba, yayin da Fulanin suka tsere daga gidajensu saboda tsoron salwantar rayukansu.

Wata majiya ta ce, jiragen da suka ka harin na karkashin Rundunar Operation Whirl Stroke wadda ke sansanin sojin saman a Najeriya da ke garin Makurdi na jihar Benue.

Kazalika wata majiyar ta ce, wasu ‘yan bindiga ne suka fara harbar jirgin saman sojin  Najeriya, abin da ya haddasa kaddamar da harin bama-baman a daukacin yankin.


Post a Comment

0 Comments