A Ranar Litinin Za A Sake Bude Nuhu Bamalli PolytechnicBbc Hausa ta labarto cewa; Hukumomin Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun sanar cewa za a sake bude makarantar domin ci gaba da karatu ranar Litinin mai zuwa.

Wata sanarwa da kakakin Kwalejin, Mahmud Kwarbai, ya fitar ranar Juma'a ta ce an dauki matakin ne saboda lamuran tsaro sun inganta a kwalejin.

“Sakamakon ingantar yanayin tsaro da kuma matakan da gwamnati jiha da hukumar makaranta suka dauka domin kare rayuka da kayayyakin da ke Kwalejin, an ba ni umarni na sanar da dalibai da ma al'ummar kwalejin cewa za a sake ci gaba da gudanar da lamura ranar Litinin, 21 ga watan Yuni, 2021," in ji sanarwar.

An dakatar da dukkan ayyuka a kwalejin ta ne bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai a makon jiya inda suka sace wasu dalibai da malamai.

Ba wannan ne karon farko da 'yan bindigar suka kai hari kwalejin ba inda suke satar dalibai da ma'aikatanta.

Jihar Kaduna na cikin jihohin da ke fama da matsalolin hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

'Yan jihar suna kokawa kan tabarbarewar tsaro a wasu yankunanta, ko da yake hukumomi sun ce suna yin bakin kokarinsu wajen tabbatar da tsaro.

Post a Comment

0 Comments