Amurka Ta Soki Gwamnatin Buhari Kan Dakatar Da Twitter


Bbc Hausa ta labarto cewa; Gwamnatin Amurka ta soki matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da Twitter a ƙasar.

Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar a yammacin Asabar, ta soki matakin tana mai cewa hakan tamkar take hakkin fadin albarkacin baki ne.

"Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da 'yancin fadin albarkacin baki. Matakin da gwamnati ta dauka a baya bayan nan na dakatar da Tuwita tamkar take 'yancin fadin albarkacin baki ne," in ji sanarwar.

A cewar Amurka, matakin ya aike da sako marar kyau ga 'yan kasa da masu zuba jari da 'yan kasuwa.

"Kamar yadda Shugaba Biden ya fada, bukatarmu ta bayyana ra'ayin kowanne mutum, da yin muhawara a bainar jama'a da yin komai a fili su ne manyan jarinmu.

Hanyar da kawai Najeriya za ta zama mai tsaro ita ce ta bari a yi sadarwa mai yawa, ba kadan ba, tare da daukar matakai na hakika wajen hadin kai, da zaman lafiya da dorewa," in ji sanarwar ta ofishin jakadancin Amurka.

A ranar Juma'a ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin na Tuwita a matsayin martani ga matakin da wasu suke ganin na goge sakon Shugaba Buhari da kamfanin ya yi ne.

Post a Comment

0 Comments