An Bai Wa Gwamnan Zamfara Tutar APC, Mataimakinsa Na Nan Daram A PDPDaga Hussaini Ibrahim, Gusau

Shugaban riko na jam'iyyar APC na kasa Mai Mala Buni ya tabbatar wa 'yan jam'iyyar APC na jihar Zamfara cewa, gwamna Bello Matawalle shi ne shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara bayan ya rushe shugabancin jihar baki daya.

Mai Mala Buni ya bayyana haka ne a wajen bikin amsar gwamna Bello Matawalle da 'yan malisar Dattawa da na wakilai da na dokokin jihar jiya a Zamfara.

Shugaban riko na jam'iyyar APC ya bayyana jindadinsa da jagorancin gwamna Matawalle da ya ke yi tare da al'ummarsa kuma suka bi shi zuwa jam'iyyar APC mai albarka a cewar Mai Mala.

A na shi jawabin gwamna Bello Matawalle ya tabbatar da cewa, zai tafi da kowa da kowa 'yan jam'iyyar APC domin samun nasarar ta da kuma bin duk hanyoyin da suka da ce wajen samun nasarar jam'iyyar.

Tsohon gwamna Abdul'aziz Yari Abubakar ya dau alwashin mara masa baya domin ci gaban jam'iyyar APC da jiha baki daya.

Sai dai kuma mataimakin gwamna Bello Matawalle, Mahadi Aliyu Gusau na nan daram a cikin jam'iyyarsa da ta bashi mukamin wato jam'iyyar PDP. 

Post a Comment

0 Comments