An Cafke Shugaban Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu

 


Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa an kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da ke son ballewa daga kasar.

Ministan Shari'ar kasar kuma Antoni Janar Abubakar Malami ne ya tabbatar da kama Mr Kanu a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Talata.

Malami ya kara da cewa an kama shugaban IPOB ne ranar Lahadi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya kan zarge-zargen da ake yi masa na neman ballewa daga Najeriya.

Daga bisani an gurfanar da shi a gaban kotu kuma ta bai wa gwamnati izinin ci gaba da tsare shi.

Kotun ta karanto masa laifukansa sannan ta É—age zamanta zuwa ranar 26 da 27 ga watan Yuli.

Kanu yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin amanar kasa lamarin da ya sa aka gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa fafutukar da yake yi wajen ganin an kafa kasar Biafra ta hanyar IPOB.

Ana zarginsa da "hada kungiyoyi na tayar da zaune-tsaye, yada labaran karya, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma shigowa da haramtattun kaya Najeriya," in ji Malami.

A watan Afrilun 2017 aka bayar da belinsa bisa dalilai na rashin lafiya sai dai ya tsere daga kasar.

A watan Maris na 2019 ne wata kotun tarayya ta soke belin da ta bai wa Mr Kanu saboda zargin tsallake belin sannan ta umarni hukumomin tsaro na ciki da wajen Najeriya su kamo mata shi.

Daga bisani ne jami'an tsaron Najeriya suka ayyana IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Malami ya ce: "Ina mai sanar da ku cewa bayan ya tsallake beli ya ci gaba da daukar matakai na tunzuru al'umma domin su yi wa kasa zagon-kasa ta hanyar amfani da kafofin watsa labarai da suka hada da talabijin, rediyo da kafofin sada zumunta."

Ya ce tunzurar jama'ar da Mr Kanu ya yi ya sa an samu asarar rayuka ciki har da na jami'an tsaro da kuma asarar dukiyoyi da ma tashe-tashen hankula musamman a Kudu Maso Gabashin Najeriya.


-Rahoton BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments