An Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Gwamnati A Wasu Biranen NijeriyaA Nijeriya an gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a wasu manyan biranen kasar, inda ta zama tashin hankali a Abuja da Legas inda ‘yan sandan suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa gungunsu.

Masu zanga-zangar dai sun yi amfani da ranar 12 ga watan Yuni dake zama ranar Dimokuradiyya a Nijeriya don bayyanawa gwamnati bacin ransu kan gazawar da suke zarginta da yi kan fannonin tattalin arziki da tsaro da kuma tsarin tafiyar da mulkin kasar.


Bayanai sun ce gabannin ranar ta 12 ga watan Yuni da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ware don girmama dan takarar shugabancin kasar M.K.O Abiola da kuma tunawa da nasarar zabensa na 1993 da gwamnatin sojoji ta soke, wasu ‘yan Nijeriya suka shirya amfani da damar wajen gudanar da zanga-zanga a fadin kasar.

Sai dai jami’an tsaro na ‘yan sanda sun kasance cikin shirin ko ta kwana inda aka girke su a wuraren da masu zanga-zangar suka shirya taruwa.


Rundunar ‘yan sandan Nijeriyar dai na kare matakin tarwatsa gungun masu zanga-zangar da cewa, ba su nemi izinin gudanar da tattakin na su ba, kamar yadda doka ta tanadar.

Rahotanni sun ce mutane sun samu fita zanga-zangar a wasu biranen sassan Nijeriyar, baya ga Legas da kuma Abuja.

Rahotanni sun ce an gudanar da zanga-zangar A jihohin Ribas da Ondo da Ogun da Osun sai kuma Filato dake arewacin kasar.

Rfi Hausa ta labarto cewa; yayin tattakin na 12 ga watan Yunin dai, masu zanga-zangar sun rika daga kwalaye dauke da rubuce rubucen adawa da gwamnati mai ci gami da neman shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda gazawarsa kan magance matsalolin da suka dabaibaye kasar.

Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da suka bayyana kansu a matsayin jagororin zanga-zangar ta baya bayan nan.

Post a Comment

0 Comments