Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kashe Dan Majalisar Jihar Zamfara Bayan Komawarsa APC

  Daga Hussaini Ibrahim, Gusau 'Yan bindiga sun kashe dan majalisar da ke wakiltar mazabar Shinkafi a majalisar dokokin jiha... Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

'Yan bindiga sun kashe dan majalisar da ke wakiltar mazabar Shinkafi a majalisar dokokin jihar Zamfara Muhammad Ahmad J.

An kashe Ahmad ne a daren Laraba a kan hanyarsa ta zuwa Kano bayan kammala taron shigar su Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara da ’yan Majalisar Dokokin Jihar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

 Babban Daraktan yada labarai na majalisar dokokin jihar Zamfara Mustapha Jafaru ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Gusau.

Honorabul J.Ahmad kafin rasuwarsa, shi ne shugaban Kwamitin Majalisar na Kudi da Kasafin Kudi.

No comments