An Yi Jana’izar Matasa 13 ‘Yan Daurin Aure Da Suka Mutu A Kano


Anyi Jana’izar matsa 13 da suka mutu a unguwar Sani Mainagge ‘yan kifi da ke karamar hukumar Gwale sakamakon hadarin mota a hanyarsu ta dawowo daga daurin aure a Zaria.

Kano Focus ta ruwaito a safiyar yau Lahadine aka gudanar da jana’izar a unugwar ta Sani Mainagge ‘yan kifi daki dari da misalign karfe 8:30 na safiya.

Dubban mutane ne daga ko ina a fadin jihar Kano suka halarci jana’izar.matasan dai su yi hadari ne da yammacin ranar Asabar bayan da motarsu ya yi taho mu gama da wata motar da ke tahowa.

Shaidun gani da ido sun ce galibin matasan nan take suka mutu, yayin da wasu suka karasa a gefen haya.

Matasan sun bar Kano ne zuwa garin Zaria domin halartar daurin auren abokinsu, sai dai a hanyarsu ta dawowa ne suka gamu da ajalinsu.


-Kano Focus

Post a Comment

0 Comments