An Yi Jana'izar Sayyida Maryam Uwargidan Marigayi Sheikh Tijjani Khalifa Zaria

 Daga Aqil Abdulkadir

Da misalin karfe 2:30 na ranar yau Talata aka gabatar da sallar jana'izar  Hajiya Maryam Uwargidan Marigayi Sheikh Tijjani Khalifa Zariya.

Har wala yau Marigayiyar ita ce mahaifiyar Hajj Murtadha Tijjani Khalifa.

Jana'izar ya samu halartar dubban mutane na nesa da kusa.

Sheikh Salahu Bn Sheikh Ibrahim Inyass  ne ya jagoranci sallar.

Manyan Shehunnan Darika na cikin garin Zariya da makwabta sun halarta.

Ita dai Hajiya Maryam ta rasu ne a yau Talata.
Post a Comment

0 Comments