An Yi Waje Da Faransa A Gasar Euro 2020

 


Switzerland ta yi waje da Faransa a gasar kwallon kafa ta Euro 2020 a daren Litinin daga bugun daga kai- sai – mai tsaron raga, bayan da suka shafe mintuna 120 suna gwabzawa.

An dai kai cikon lokaci wasan yana 3-3 ne, aka kuma shiga karin lokaci ba ta sake zani ba, lamarin da ya kai su ga bugun fenariti.

A farkon wasan, Switzerland ne suka fara saka kwallo a raga,  Faransa suka farke ta hannun Karin Benzema, suka kuma shiga gaba da 3-1, amma Switzerland suka yunkuro har aka kai cikon lokaci 3-3.

A bugun daga kai sai mai tsaron raga, Kylian Mbappe ne ya baras da nasa, bayan da ya buga mai tsaron ragar Switzerland, Yann Sommer ya tare, aka tashi 4-5.

Sai dai a ganawar da ya yi da manema labarai bayan wasan , kyaftin din tawagar kwallon kafar Faransa, kuma mai tsaron raga Hugo Lloris ya bayyana goyon baya ga Mbappe, yana mai cewa nasara da akasinta duk tasu ce.


Post a Comment

0 Comments