Daga Muh’d Shafi’u Saleh Tsohon matainakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya fadada kamfanin kasuwancinsa, ta hanyar samar da sabon ka...
Daga Muh’d Shafi’u Saleh
Tsohon matainakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya fadada kamfanin kasuwancinsa, ta hanyar samar da sabon kamfanin saka Buhuna da tsirrai (New Woven Sacks Factory and a Shrink Laminate Plant), a Yola.
Sabon kamfanin da yake karkashin kamfanin Adama Beverages, shine na biyar da ke karkashin tsohon matainakin shugaban kasar a jihar Adamawa.
A jiya litinin tsohon matainakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya jagoranci bude kamfanin dake kan hanyar Numan a garin Jimeta, da gwamnan jihar Ahamadu Umaru Fintiri, ya kaddamar da fara aikin kamfanin.
Da yake jawabi lokacin bude kamfanin gwamna Ahamadu Fintiri, ya ce “gwamnatinmu zata kirkiro da ingantacciyar yanayi ga kamfanoni domin su bunkasa” inji gwamna Fintiri.
Gwamnan ya kuma nuna godiya da farin ciki bisa kirkiro da masana’antun da tsohon matainakin shugaban kasar yayi a jihar da samar da ayyukan yi ga dubban jama’a.
Tunda farko da yake jawabi shugaban gudanarwar kamfanin Shehu Atiku Abubakar, ya ce sabon kamfanin saka buhunan, zai iya samar da buhuna sama da miliyan tara a kowace shakara.
Ya ci gaba da cewa “yanzu zai tsara ya samar a baya, zai samar da buhu ga daya daga cikin kamfanonin Priam Group, Rico Gado Nutrition Nigeria.
“Kafin wannan lokacin Rico Gado, na samun duk buhuna ne daga Lagos, amma yanzu dari bisa darin buhunan da Rico Gado ke bukata ya samu daga Priam Group” inji Shehu.
Haka Kuma shugaban kamfanin ya ce manufar samar da kamfanin shine magance matsalar ingantaccen buhu da manoma ke fuskata a jihar dama sassan jihohin Nijeriya.
-LEADERSHIP A YAU
No comments