‘Ba Da Gaske Gwamnatin Ganduje Take Ba Kan Muhawara Da Sheikh Abduljabbar’

 Shugabannin zauren hadin kan Malaman Jihar Kano sun ce sun fuskanci 'ba da gaske gwamnatin Ganduje take ba kan muhawara da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara' kamar yadda BBC Hausa suka labarto.

Yayin wani zama da suka yi wanda Dakta Saidu Dukawa wanda daya daga cikinsu ya wallafa a shafinsa na Facebbok, yace sun fitar da matsaya game da jan kafar da gwammatin Kano ke yi kan zaman da aka fara tsarawa na tuhumar da za a yii wa Sheik Abduljabbar Naisru Kabara na zargin 'cin zarafin da ya ke yi wa Manzon Allah da Sahabbansa'.

Sun yi bayanin matakan da suka dauka a baya na rubuta wa gwamnati wasika har guda uku, daya zuwa ga hukumar shari'a daya kuma zuwa ga kwamishinan sharia, guda kuma zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano Ganduje kai tsaye.

Dukawa ya rubuta cewa "amman tsawon wata uku babu amsar ko daya daga ciki wasikun, a don haka, Malaman sun bukaci duk wanda ya ke neman bayani game da maganar to ya nema a wurin gwamnati" Dukawa ya rubuta.

Haka kuma an bukaci "al'umma su dukufa da addua cewar duk wanda ya taba mutuncin sahabbai da wanda ya goyi bayansa, Allah Ta'ala ya yi mana maganinsa".


Post a Comment

0 Comments