Shugaban majalisar wakilai a Najeriya ya bayyana bukatar a sauya kundin tsarin mulkin Najeriya. Ya bayyana cewa, ba a rubuta kun...
Shugaban majalisar wakilai a Najeriya ya bayyana bukatar a sauya kundin tsarin mulkin Najeriya. Ya bayyana cewa, ba a rubuta kundin tsarin cikin natsuwa ba, wannan yasa ake da matsaloli da yawa. Ya bukaci hadin kan 'yan Najeriya da goyon bayansu kan aikin sauya kundin tsarin mulkin kasar.
Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya gaza magance wasu manyan matsaloli da ke addabar kasar, abin da ya sa kenan 'yan majalisa suka yanke shawarin sauya shi, BBC Hausa ta ruwaito.
Gbajabiamila ya fadi hakan ne a wajen taron jin ra'ayoyin jama'a kan sauya kundin tsarin mulkin a Legas a ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa majalisar wakilan shawara kan yada labarai ta fitar. Shugaban majalisar ya ce kundin tsarin mulki ba wai tushen kasa ba ne kawai, kamata ya yi ya zayyana ka'idojin zaman kasa da kuma burikanta na akida da gaskiya, amma "namu kundin tsarin mulkin na cike da nakasu," a cewar Gbajabiamila.
No comments