Babu Wanda Zai Bar Jami'ar Jihar Kaduna Saboda Bai Biya Kuɗin Makaranta Ba -Farfesa TankoShugaban Jami’ar Jihar Kaduna ya kawar da tsoron da iyayen ɗalibai suke da ita game da ƙara ƙudin makaranta inda ya tattauna da manema labarai ya ce sun yi tsari mai kyau ta yadda babu wani ɗalibin da zai bar makaranta saboda bai biya kuɗin makaranta ba. 

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da ‘yan jaridu game da kara kudin makaranta
 
TAMBAYA: Jama’a sun ga sanarwar kun rufe makaranta cewa, masu digiri su zauna a gida har zuwa wani lokaci. Ko me ya kawo haka?

AMSA: Kamar yadda jama’a suka sani an kara kudin makaranta, wanda hakan ya sa dalibai suka dinga yin zanga-zanga. Saboda gudun kada a samu matsaloli wanda duk lokacin da ake zanga- zanga cikin wannan yanayi kada ya zo a kai ga har an rasa rai. Saboda haka ne muka yanke shawara maimakon mu bar yara su dinga yin zanga zanga, gara mu kulle makarantar kowa ya zauna hankalinsa ya dawo sannan mu dawo mu zauna mu tattauna.
 
TAMBAYA: Shin wannan kulle makarantar ba ku tunanin zai shafi karatun yara musamman la’akari da kwanan nan aka dawo daga hutun annobar Korona Bairos?

AMSA: Dalili shi ne in aka bari yar ana zanga-zanga, wasu zauna gari banza suna iya shiga cikin daliban nan su bata abin. To, kuma ta haka sai ka an kai ga rasa rai. To abin da muke gudu kenan, kuma ka ga ya fi a kulle makarantar har kowa ya samu natsuwa da ce an samu asarar rayuka da dukiyoyi. Bayan an samu natsuwa sannan mu bude makarantar sai a zo a ci gaba da karatun cikin natsuwa. In ba a zaman lafiya, karatu ba zai yiwu ba.
 
TAMBAYA: A matsayinku na hukumar makaranta, ba ku yi wani kokari ba ne na ganin kun zauna da yaran nan domin ku fahimtar da su ga dalilin da ya hukumar makaranta ta kara kudin makaranta?

E, mun zauna da dalibai kamar yadda aka sani mun zauna da shugabannin dalibai, mun zauna da daliban nan musamman wadanda suke zanga-zangar. Abin da muke cewa shi ne, akwai hanyoyi wanda aka yi wanda za su taimaka. Wanda ba shi da ikon biya, a taimaka masa ya biya. Mun kawo tsare-tsare wanda in har dalibai suka bi shi in Allah ya yarda babu wanda zai bar makaranta wai domin ba shi da kudin biyan kudin makaranta. Abin da muka tabbatar wa dalibai kenan. Matsalar yanzu ba tasu ba ce. Matsala ce ta iyaye, kuma mu ne iyayen domin haka dukkaninmu za mu sa hannu domin ganin an magance wannan matsalar.

Da a ce ba a kara kudin makarantar nan ba, abin da kuma ya kamata a koya maka ba a koya maka ba saboda makaranta ba ta da kudin da za ta iya maka, gara a kara din ya zama an iya ba ka abin da ya kamata din wanda in ka fita za a ce wannan ya samu ilimin da ya dace shi.
 
TAMBAYA: A cikin jawabinka ka yi magana cewa akwai hanyoyi da kuka fito da su domin ganin an tallafa wa wadanan nan yaran nan saboda su samu su iya biyan wannan kudin makaranta. Wasu irin hanyoyi ne wannan?

AMSA: Na farko dai akwai tallafin karatu wanda ake kira ‘scholarship’. Wanda a ‘scholarship’ din ma kala biyu; akwai wanda ake ba masu karamin karfi. Akwai na masu kokari da kuma ma wanda ake ba da bashi wato ‘loan’.

Bayan nan kuma mun tattauna da shugabannin kananan hukumomi sun tabbatar mana za su taimaka wa daliban da suka fito kananan hukumominsu saboda su biya kudin makarantar nan.
Sannan bayan haka kuma, mun tattauna da kungiyoyi masu zaman kansu kuma muna fatan za su taimaka wa musamman mata wadanda  ba za su iya biya ba. Akwai kungiyar mata da suka ce za su taimaka wa mata.

Bayan nan kuma, akwai kungiyoyi na makaranta irinsu Majlis da SPSS da sauransu wadanda su ma suka yi alkawarin tallafa wa wadanda suka kasa biyan kudin makaranta. Saboda haka in dalibai suka yi hakuri, komai zai wuce. Dalibai su yi hakuri kwanan nan za mu bude ‘portal’ inda duk wanda ba zai iya biya ba zai je ya bude ya sanya sunansa.
Ya kamata dalibai su gane, matsalar ba tasu ba ce. Su mu hada hannu mu ga yadda za a yi kowa ya iya biyan kudin makaranta. Amma idan aka ce a yi ta zanga-zanga , ku ba za ku samu yadda kuke so ba, mu ma ba za mu samu yadda muke so ba. Saboda haka sai ka ga gaba daya an bata koma daya ba ta gyaru ba.
 
TAMBAYA: Ka yi maganar wani wuri da za a bude ‘portal’ domin duk wanda ba zai iya biyan kudin makaranta ba ya sanya sunansa. Wadanda a za su iya biya ba ne za su sanya sunansu a ciki?
 
AMSA: Duk dalibin da yake ganin ba zai iya biya ba zai sanya sunansa a ciki. Daga baya kuma akwai shugaban dalibai shi zai tantance, e lallai wane ba zai iya ba. To sai kuma mu ga a ina ne zai iya samun tallafi? Ta kungiyar mata ne ko kuma ta karamar hukuma ne ko kuma ta kungiyar da ke cikin makaranta ne?
 
TAMBAYA: Akwai masu tambaya cewa wai dole ne sai an kara kudin makarantar nan. Ko kuma wasu dalilai ne hukumar makarantar take ganin ya kamata a kara kudin makaranta?
 
AMSA: Wato yanzu ka ga shekaran bara an ba mu miliyan dari hudu da ashirin. Bara wancan an ba mu miliyan dari biyar da tamanin. Amma bana gaba daya miliyan arba’in aka ba mu a matsayin kudin gudanarwa, wato ‘overhead cost’. To miliyan arba’in me zai yi? Komfyutocin nan da kake gani dole sai ana siyan musu abubuwa. Sannan ko jarrabawar da za a yi sai an siyo takarun jarrabawa.

Ba yadda za a yi a gudanar da jami’a in ba isassun kudi. Saboda miliyan arba’in din da aka ba mu bai wuce mu kashe shi a wata daya ba wurin gudanar da jami’ar .
Saboda haka nake cewa idan dalibi an dauke ka an ce za a koya maka a ba ka takardar sheda cewa ka yi digiri a komfyuta ko a micro biology Ka je dakin gwaje gwaje ba kayan da za ka koyi aikin da shi. In kuma kana koyon aikin likitanci ba a je an siyo gawa da za ka zo ka yi aiki a kanta, to wane likita za ka zama? Ka ga dole ne jami’a sai da kudi kuma gwamnati ta kasa saboda karancin kudin shiga, ba kudin da za ta bayar wanda zai wadaci jami’a. shi kan shi wannan din ko an bayar ba wai zai iya daukan nauyin jami’an ba ne zai dai taimaka ne kawai.
 
Abdullah Yunus Abdullah
abdullah.yunus@kdsg.gov.ng

Post a Comment

0 Comments